Akwai yiyuwar nan gaba kaɗan Ganduje ya dawo jam’iyyar PDP – Sule Lamido
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Tsohon gwamnan Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya yi hasashen samun ɓaraka mai ƙarfi a cikin jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce nan ba da jimawa ba manyan jiga-jigan jam’iyyar ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje na iya komawa jam’iyyar PDP.
Sule Lamido ya yi wannan ikirarin ne a yayin taron jam’iyyar PDP a ɗakin taro na Aminu Kano da ke Dutse a jihar Jigawa.
KU KUMA KARANTA:Najeriya ka iya zama kamar China idan aka koma tsarin jam’iyya daya – Ganduje
“Na tabbata waɗanda suka bar PDP za su dawo, domin APC cike take da rikici kuma nan bada dadewa ba gayyar zata watse” in ji Lamido.
Ya cigaba da cewa “Ku rubuta ku ajiye, nan da watanni shida, da yawa daga cikin waɗanda suka koma APC za su sake dawo PDP, kuma idan suka yi hakan, PDP za ta ƙara karfi mu karɓe mulki a shekarar 2027.