AIG Madaki ya kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga

0
616

Daga Fatima GIMBA, Abuja

A Madaki mataimakin Sufeto Janar (AIG) mai kula da shiyya ta 12 (wanda ya ƙunshi jihohin Bauchi da Gombe) mai hedikwata a Bauchi. A yau ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a Bade, jihar Kaduna, a hanyarsa ta zuwa Abuja domin ganawa da manema labarai.

Neptune Prime ta tattaro cewa AIG Madaki ya samu rauni da harbin bindiga a ƙafarsa yayin da mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) Gideon, mai bin umarninsa, aka kashe sannan aka harbi direbansa a hannu.

Gideon, wanda kwanan nan ya samu mukamin ASP ya taɓa yin aiki tare da marigayi Ali Kwara.

Leave a Reply