Abin da ya sa ‘yan bindiga suka kai wa tawagata hari – Sarkin Birnin Gwari

0
332

Daga Rabo Haladu
Sarkin Birnin Gwari Alhaji ZubairuJibril Mai Gwari II ya ce ‘yan bindigar da suka kai hari kan ayarin motocinsa sun yi niyyar halaka shi ne.

Sarkin ba ya cikin ayarin motocin nasa, wadanda suke kan hanyar zuwa birnin Kaduna domin yin taro da gwamnan jihar, lokacin da aka kai musu hari inda aka yi kaca-kaca da motarsa.

A hirar da ya yi da manema labarai  Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce shi aka nufa da harin amma aka kuskure.Ya kara da cewa yana tsammanin akwai hadin bakin wasu mutane da ke garin Birnin Gwari a wajen kai wa ayarinsa hari.Ya ce: “Akwai kyakkyawan zato cewa [‘yan bindigar] ba za su yi wannan abu ba sai da taimakon wasu. Ka ga idan ka dubi motata, ai ka ga sun yi niyya ne su yi kisan kai, domin ka dubi gilas din gaba sun yi ratata da shi. Daidai wurin da na zauna, an fasa gilas din da harsashin bindiga. Hakan na nufin sun yi niyyar su kashe mu ne. Irin wannan kuma ba ka fid da zaton cewa akwai wasu suna nan a cikin gari duk abin da ake yi suna gaya musu.”

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce an yi sa’a ba samu asarar rai ba, kawai fargaba ce irin ta dan adam da dole sai da suka sha magani daga baya suka samu waraka.

Rawar da gwal ke takawa

Sarkin ya ce wasu suna ganin ma’adinan zinaren da ke karkashin kasa a yankin na cikin abubuwan da suka sa aka tsananta kai hare-hare a yankin nasu.

“Da yawa na cewa ma’adanin gwal da muke da shi ne ya ja muka samu kanmu cikin wannan rikici, to me ya sa ba za a je a nemi gwal din ba a rabu da mu, sai a yi ta kashe mu a hana mu ci gaba,” in ji Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II.

Tun 1994 Birnin Gwari ke fama da matsalar tsaro

Ya ce mutanen Birnin Gwari masu kaunar zaman lafiya ne kuma suna fatan ya dore kamar yadda suke a baya.

“Mun fi shekara 20 da wani abu muna fama da wannan matsala, kuma ta fara ne da satar shanu tun kusan 1994. Da abin ya yi gaba sai suka fara fashi, har sai da mutanen Binin Gwari suka fara sanya kudin ‘yan fashi a aljihu idan za su yi tafiya, saboda in suka nemi kudi suka rasa a wurinka zai iya kai wa ga kisa ko kuma su yi wa mutum dukan kawo wuka,” in ji Sarkin.

A cewarsa bayan sun gama sace shanun, mutane sun koma kare kansu sai suka fara tunanin wata hanyar ta daban da za su fara amfani da ita sai suka koma satar mutane.

Wannan ne sanadin da ya ja sama da shekara 20 babu wani aikin ci gaba a Birnin Gwari saboda wurin babu tsaro don haka babu wanda zai samar da wani abin more rayuwa a yankin.

Mafita kan wannan matsala

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce babbar mafita ga matsalolin da ke addabar yankin ita ce mutane su “koma ga Allah, ya fada cewa babu wani abu da zai sauya sai in har ba mu muka fara sauyawa ba.”

Ya ce babu mamaki an yi wa Allah wani laifi ne shi ya sa ya jarrabe al’umma da wannan masifa, amma idan aka koma aka tuba sai komai ya daidaita.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro a Najeriya kuma musamman a yankin arewaci.

Kazalika Birnin Gwari na daya daga cikin wuraren da wannan tsaro ya fi tabarbarewa a cikinsu, wanda da wuya a yi mako guda ba a kai hari ko an sace wani ba a yankin

Leave a Reply