Ɗangote ya ware Naira Biliyan 15 domin bunƙasa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil
Ɗangote ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyar da jami’ar ta gudanar a ranar Asabar, inda ya ce wannan kuɗaɗe na daga cikin wani shiri na ci gaba na tsawon shekaru biyar da jami’ar ke shiryawa domin ɗaga darajarta ta kai matakin jami’o’in Duniya.
KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya bawa ɗaliban da suka kammala karatu da mafi ƙoluluwar daraja a Jami’ar Ɗangote da ke Wudil aiki
Daga cikin muhimman ayyukan da za a aiwatar da kuɗaɗen sun haɗa da gina sabbin ɗakunan kwanan dalibai da ɗakunan gwaje-gwaje na sashen Injiniya, gina katafaren ɗakin Computer na zamani ɗauke da intanet na awa 24 a kullum, gina sabon ginin majalisar jami’ar (Senate Building).
Haka kuma za’ayi amfani da kudaɗen wajan ɗaukar ɗaliban da suka yi fice a bangaren injiniya bayan kammala hidimtawa kasa don cigaba da horar da su.