Ɗangote ya karya farashin dizel zuwa N1,000 kan kowace lita

0
106

A wani yunƙuri na rage wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta, matatar man Aliko Ɗangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizel daga naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita.

A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Talata ya ce ana sa ran ”rage farashin man dizel ɗin zai yi tasiri sosai a dukkan ɓangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.”

A watan Janairu ne matatar man Dangote ta fara samar da man dizel da na jiragen sama.

Tun daga lokacin matatar take sayar da man dizel a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 a kowace lita, kimanin kashi 30 cikin 100 na ragin farashin kasuwa da ya kai kusan naira 1,600 kan kowace lita.

A ranar 12 ga watan Disamba 2023 ne kamfanin ya amshin jirgin ɗanyen mansa na farko daga ɗanyen mai na Agbami na kamfanin Shell International Trading and Shipping Company Limited (STASCO), ɗaya daga cikin manyan kamfanonin kasuwanci a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, wanda ke cinikin ɗanyen mai sama da ganga miliyan 8 a wacce rana.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

Kamfanin ya ɗaura ɗamarar fara samar da tataccen man fetur tare da samun ƙarin ganga miliyan ɗaya na ɗanyen man da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC Ltd) ya kawo.

A farkon watan ne kamfanin ya fara fitar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here