Ɗangote ya bawa ɗaliban da suka kammala karatu da mafi ƙoluluwar daraja a Jami’ar Ɗangote da ke Wudil aiki
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugabanin rukunin kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewar ya tsara gudanar da ayyukan cigaban jami’ar Aliko Dangote, da garin wudil na naira biliyan 15 domin cigaban makarantar a shekaru biyar.
KU KUMA KARANTA: Gidauniyar Ɗangote ta ƙaddamar da rabon abinci na naira biliyan 16 ga talakawa
Dangote ya bayyana hakan yayin bikin yaye dalibai karo na biyar a yau asabar Wudil, inda ya bayyana daukar aiki a kamfaninsa ga daliban da suka zamo na daya a jami’ar.
Yakara da cewar gidauniyarsa zata gina gurin kwanan dalibai na zamani da dakin karatu da sauran kayayyakin karatun dalibai a makarantar.