Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Carlo Ancelotti na kungiyar Madrid ya tabbatar da barin ƙungiyar
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Carlo Ancelotti ya tabbatar da barin Madrid don karɓar aikin horas da tawogar ƙwallon ƙafar Brazil
Carlo Ancelotti ya tabbatar da cewa zai karbi ragamar horar da tawogar ƙwallon ƙafar kasar Brazil a hukumance a ranar 26 ga watan Mayu, wanda hakan zai kawo ƙarshen zaman sa a matsayin kocin Real Madrid.
KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta ɗaure mai sana’ar kwalliya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira
Da ya ke magana a yau Talata, Ancelotti ya yi karatun baya game da zamansa a Real Madrid ta ƙasar Spain kuma ya yaba wa tsohon dan wasa kuka wanda zai gaje shi wajen horar da kungiya, Xabi Alonso.
“Xabi Alonso baya bukatar wata shawara daga gare ni a matsayinsa na babban mai horaswa Yana da komai don zama babban koci,” a cewar Ancelotti.