Ɗan takarar Sanatan APC a Yobe ta gabas, ya yiwa al’ummomin Geidam da Yunusari alƙawarin morar romon dimokuraɗiyya 

0
91

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Ɗan takarar neman cike gurbin kujerar ɗan majalisar dattawa a mazaɓar jihar Yobe ta Gabas, a ƙarƙashin jam’iyyar APC Honarabul Musa Mustapha (Kulas) ya ba da tabbaci ga al’ummar yankunan ƙananan hukumomin Geidam da Yunusari kan cewar lallai da zarar sun zaɓe shi ya faɗa zauren majalisar dattawan ƙasar nan a zaɓen cike gurbin da ke tafe lallai za su sharɓi romon dimokuraɗiyya.

Alhaji Musa ya furta haka ne yayin gangamin yaƙin neman zaɓen sa a garuruwan Geidam da Yunusari a ranar Asabar a cikin rangadin da suke yi a ƙananan Hukumomin mazaɓar 7 haɗe da tawagar yaƙin neman zaɓen ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar dokokin Jihar Yobe da shugaban jam’iyar APC a jihar Yobe Alhaji Muhammadu Gadaka da Sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga yankin da ma sauran sassa daban-daban na jihar.

A yayin yaƙin neman zaɓen a ƙananan hukumomin na Geidam da Yunusari da aka gudanar a baya bayan nan, ɗan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC, Honarabul Musa Mustapha, ya yi alƙawarin kawo wa al’ummar yankin ribar dimokuraɗiyya idan an zaɓe shi a zaɓen da ke tafe na cike gurbi a mako mai zuwa 3 ga wannan watan Fabarairu.

KU KUMA KARANTA: An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen maye gurbin Sanatan Yobe ta Gabas

Da suke jawabi shugabannin Jam’iyyar ta APC daga sassan biyu sun ba da tabbaci ga ɗan takarar cewar, za su ba shi  ƙuri’u masu yawan gaske, sun kuma buƙaci ɗan takarar da ya himmatu wajen kawo ayyukan raya ƙasa a yankunan a idan aka zaɓe shi musamman kan abin da ya shafi samar da aiki ga matasan yankunan tare da samarwa da ƙananan ‘yan kasuwa jari.

Haka nan al’ummar yankunan kasancewar su manoma ne sun nemi ɗan takarar da zarar ya je majalisar ta dattawa to kuwa kar ya manta da manoman wajen samar musu da kayayyakin yin noma da makamancin haka.

Tun farko da ya ke jawabi kakakin majalisar dokokin jihar Honarabul Buba Mashio ya tabbatar da cewar lallai wannan ɗan takarar na su mutum ne mai hangen nesa da zai musu wakilci nagari wadda ya roƙi al’ummomin yankunan na Geidam da Yunusari da su ba shi goyon baya a zaɓen cike gurbin da ke tafe a  mako Mai zuwa.

Haka nan shi ma shugaban Jam’iyyar ta APC a jihar Yobe Alhaji Muhammadu Gadaka ya nemi al’ummar yankunan biyu da kar su yi ƙasa a gwiwa wajen zaɓen Honarabul Musa Mustapha don cike gurbin wannan kujera ta majalisar dattawa a mazaɓar ta gabashin Yobe.

Leave a Reply