Ɗan shekara 15 ya ƙera masallacin Ka’aba ya ƙayatar da ‘yan Najeriya

0
650

Aji Bukar Hazuƙin matashin ɗan Najeriya ne mai shekaru 15 dake zama a Maiduguri, babban birnin jihar Borno wanda ya ƙayatar da ‘yan Najeriya da hazaƙarsa.

Matashin yaron ya ƙirƙira tare da ƙera ƙaramin Masallacin Makka wanda yayi sak da na Saudiyya kuma hotunan sun bazu tare da birge jama’a a Najeriya dama sassan duniya.

Wannan fasaha ce da ba kowa ke da irin ta ba saboda jama’a da dama sun dinga yabawa matashin yaron wanda suka ce zai dace da fannin ƙere-ƙere.

Jama’a sun bayyana yadda ya matuƙar birge su ganin cewa yaron bai bari hazaƙarsa ta dishe ba duk da shekarun da aka ɗauka babu zaman lafiya a yankinsu.

Leave a Reply