Ɗan sanda ya yima ƴar ƙanwarsa ciki’ a Jihar Nasarawa

0
585
GOMA, DRC - APRIL 2008: Unnamed Girl, 14 years old: we were in Kabaya because of the war, and I was going to take food. Three soldiers--they were Nkunda's men (I know because they were very tall, they were Tutsis) and they raped me. I bled. They put us in a house , and we ran away, but they followed us and took us to another house. Four had guns, one did not. Three men raped me. I was screaming and crying, but they raped me. I tried to walk with difficulty the next day. Then i came here. My parents and I are in this camp (Kibomba). It happened one month ago, and when i told my parents, they didn't insult me, and they told me to come here (Heal Africa) and get medicine. Congolese women who were sexually assaulted in North Kivu, in Eastern Congo, April 12, 2008. An average of 400 women per month were estimated to be sexually assaulted in the autumn of 2007 in eastern Congo, while in the first months of 2008, the figure dropped to an average of 100 women per month. This said, many women never make it to treatment centers, and are not accounted for in these statistics. (Photo by Lynsey Addario/Getty Images Reportage)

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta damƙe wani jami’inta mai muƙamin insifekta, kan zargin yi wa wata ‘yar kanwarsa, ‘yar shekara 15 fyade, da yi mata cikin shege a Jihar Nasarawa.

An kuma kama wasu mutum uku, ciki har da wani likita, dangane da wannan aika-aika.

Ƙungiyar mata lauyoyi ta Najeriya, wato FIDA, wadda ta bankaɗo labarin afkuwar wannan lamari, ta ce za ta ci gaba da bin diddigin batun, har sai ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi a al’amarin.

Bayanan da BBC ta tattaro daga harabar hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, sun nuna cewa an damƙe jami’in ɗan sanda mai mukamin sufeto, wanda ke aiki a sashen tattara bayanan sirri a wannan runduna.

Reshen Jihar Nasarawa na kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya ce ta bankado labarin wannan aika-aika, kuma take ta bibiyar lamarin.

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra, wadda ita ce shugabar ƙungiyar FIDA reshen Nasarawa ta bayyana cewa tun da farko sun samu rahoto ne daga wata cibiya ta tabbatar da adalci da zaman lafiya inda suka yi masu bayani kan wannan lamari.

“Da muka samu wannan labarin sai muka je B division a nan garin Lafiya muka je muka tarar da ƴan sanda sa’annan aka kama insifekta ɗin da matarsa da ɗansa,” in ji Barista Rabi’atu.

“Sai muka kai yarinyar asibiti aka je aka yi gwaji aka tabbatar tana da ciki wata shida amma kuma an so a zubar da cikin, ɗan da ke cikinta ɗin ya mutu har kwana uku yana cikinta.

Ta bayyana cewa a rana ta uku ce suka kai ta asibiti inda har ta haifi ƴa mace wadda tuni ta mutu a ciki inda ta ce jaririyar har ta soma ruɓewa.

Barista Rabi’atu ta ce yarinyar ta tabbatar cewa ɗan sandan ne ya yi mata ciki inda ta ce yakan dawo gida da lemu ko wani abin sha, amma ashe yana zuba mata wani magani ne a ciki, wanda duk lokacin da ta farka daga bacci sai ta ga jikinta duk ya ɓaci da jini.

A cewarta, sai daga baya yarinyar ta ankara ta gano cewa kawunta ne ke kwana da ita.

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra ta ce, ƙungiyarsu ta FIDA ta lashi takobin yin tsayuwar daka, wajen ganin an gurfanar da masu laifi a lamarin, a kuma hukunta su, domin hakan ya zama wani kakkausan gargadi ga wasu.

Leave a Reply