Ɗan Najeriya wanda ya mayar wa makarantar sa satifiket, ya samu tallafin N500,000

1
993

Mista Alaba ya ce idan har ya samu aka dawo masa da kuɗaɗensa da ya kashe lokacin yana ɗalibi, zai iya bunƙasa basirar sa. Mr Alaba ya kammala karatunsa na Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomosho, Jihar Oyo, Osunleke Alaba, wanda kwanan nan ya mayar wa makarantar satifiket dinsa, ya kuma nemi a mayar masa da kuɗinsa a lokacin da yake karatun. Ya samu tallafin N500,000 daga asusun ƙungiyar tsofaffin daliban makarantar.

.”Mista Alaba, wanda ya kammala karatunsa a Sashen Noma da Raya Karkara, ya koka kan “rashin darajar” takardar kammalawar, biyo bayan kasa samun aiki shekaru bayan kammala karatunsa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, Mista Alaba ya tada jijiyar wuya a ɗaya daga cikin gine-ginen makarantar, yana mai cewa iyayensa sun riga sun gaji da dogaro da yake yi da su har yanzu.

Ya ce idan har ya karɓi kudadensa da aka caje shi tsawon shekaru biyar, zai iya amfani da shi don bunƙasa fasaharsa ta hanyar da ya dace. “Na mayar da takardar shaidar ne saboda ba ta da wani tasiri a rayuwata. Na nemi a mayar mini da kuɗin da aka biyamin a makaranta don in yi amfani da shi don gina hazaƙa ta da kuma rayuwa mai ma’ana. “Ni ɗan wasan barƙwanci ne, kuma har ma na ci lambar yabo ta MTN a lokacin da nayi bautar ƙasa a 2016.”

Mahaifin ’ya’yan biyun ya ci gaba da cewa duk da ƙoƙarin da yake yi na kyautata rayuwar iyalinsa, ya ci gaba da samun shawarwarin ya shiga harkar tsafi don ya zama mai arziki, “amma ba zan taɓa yin hakan ba.”

“Mahaifina yana da shekara 90 amma ina ci gaba da karɓar bashi daga gurinsa maimakon in ba shi. Abin da nake nema a yanzu shi ne taimako ta kowace hanya don in ci gaba da sana’ar nishadantarwa. Ba na son aikina ya lalace.”

Martani

Ƙasa da mako guda da faifan bidiyon na buƙatarsa ​​mai ban mamaki ya bazu a shafukan sada zumunta, ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar ta kawo masa dauki. A wani sabon saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Alaba ya ce ƙungiyar tsofaffin daliban ta miƙa masa chak na Naira 500,000. Yace; “Na yi amfani da wannan kafar ne domin in nuna matuƙar godiyata ga ƙungiyar Global Body of LAUTECH Alumni kamar yadda shugaban ta, Hon. Onilede Solomon wanda aka fi sani da LIMO, kwamitin amintattu na ƙungiyar reshen jihar Oyo, ya gabatar mani chekin #500,000 a yau.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da kasancewa tare da ku da dukkan membobin ƙungiyar don nuna soyayya da goyon baya. Na gode sosai da sosai.

1 COMMENT

Leave a Reply