Ɓarawon da kotu ta ɗaure saboda sata ya kuma yin sata jim kaɗan bayan da aka sako shi

2
548

An kama wani tsohon mai laifi, Yakub Yusuf, mai shekaru 23, bayan an sako shi daga gidan yari.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Alhamis, ‘yan sandan karta kwanan ta rundunar RRS ne suka kama Yusuf a safiyar ranar Asabar, bayan an sake shi daga gidan yari a ranar Juma’a. Hakan ya faru ne bayan wata ƙungiya mai zaman kanta ta biya tarar da kotu ta aza masa bayan da aka same shi da laifin sata a gidan wani mai na jihar Legas, da ke Alausa a ranar 1 ga watan Nuwamba.

A ranar Asabar ne aka sake kama Yusuf bayan ya kutsa cikin harabar hukumar kashe gobara ta jihar Legas. A wannan karon, ya saci murfin bawul na tsohuwar motar kashe gobara a wanda ake kan aikin gyaransu.

2 COMMENTS

Leave a Reply