Ƴan sandan Turkiyya na ci gaba da kama ƴan ta’addar Daesh

0
183

Turkiyya ta kama ƴan ta’addar Daesh 20 a birnin Istanbul da wasu sauran garuruwan kasar.

An yi kamen ne bayan umarnin da aka samu daga ofishin Mai gabatar da ƙara na Istanbul kan a kama mutum 14 da ke da alaƙa hedkwatar Daesh da ke Dashisha a arewa maso-gabashin Siriya, in ji majiyoyin tsaron da suka nemi a ɓoye sunayensu saboda ba a ba su damar magana da kafafan yaɗa labarai ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya a ranar Larabar nan ya fitar da sanarwa ta shafin X cewa “Ƴan sandan Turkiyya sun kama mutum 20 a larduna bakwai yayin kai farmakin “Bozdogan-26″ da ake ƙaddamarwa kan ƴan ta’addar Daesh.”

Ya jaddada cewa “Tare da addu’o’i da goyon bayanku, ba za mu ja da baya ba a yayin da muke ci gaba da zage damtse wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da goyon baya ga ƙasarmu har sai an ga bayan ɗan ta’adda na ƙarshe.”

Turkiyya ya tsananta kai farmakai kan ‘yan ta’addar daesh bayan da ƙungiyar ta kai hari kan cocin ‘yan Italiya a watan Janairu a lokacin bauta tare da kashe mutum guda.

Tun 1 ga watan Yunin 2023 jami’an tsaron Turkiyya ke ƙaddamar da farmakai kan ‘yan ta’addar Daesh inda aka kama sama da su dubu biyu

Turkiyya ta kasance ƙasa ta farko a ta ayyana Daesh a matsayin ƙungiyar ta’adda a 2013, ta fuskanci hare-hare da dama daga ƙungiyar.

Sama da mutum 300 ne suka mutu yayin da wasu ɗaruruwa suka jikkata sakamakon hare-haren na ‘yan ta’addar Daesh da suka haɗa da na ƙunar baƙin wake 10, na bam bakwai da na bindigu huɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here