Ƴan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin ‘yan kasuwa da na sojojin dake rakasu, a jihar Katsina

1
662

Rahotanni daga jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani ayarin motocin ‘yan kasuwa, da na sojojin da ke musu rakiya.

Wani rahoton na cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu, kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a san inda wasu sojojin suka shiga ba.

Harin ya auku ne tsakanin ƙauyen Shimfida da garin Jibia, wurin da ke fuskantar karuwar hare-hare daga barayin daji a ‘yan makonnin da suka gabata.

1 COMMENT

Leave a Reply