Ƴaƴan kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano su 15 na tuhumar Shugabannin su da laifin ha’intar su

0
97
Ƴaƴan kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano su 15 na tuhumar Shugabannin su da laifin ha'intar su.

Ƴaƴan kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano su 15 na tuhumar Shugabannin su da laifin ha’intar su

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ƴaƴan ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai na ƙasa reshen jihar Kano, sun rubuta takardar ƙorafi kan shugabannin ƙungiyar bisa zargin saɓa wa kundin tsarin mulki, zargin da ke da alaka da karkatar da kudade.

Takardar ƙorafin mai kwanan wata, 1 ga Mayu, 2025 ta samu sa hannun guda cikin ƴan ƙungiyar Abdulmumin Murtala a madadin wasu mambobi 15 da aka kora.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin inganta aikin jarida a jihar

Kwafin takardar koken da sakataren ƙungiyar Mustapha Hodi ya tabbatar da cewa ya samu, mambobin ƙungiyar ne suka raba ta wa ƙungiyar ranar Juma’a.

A cewar ƙorafin, daga cikin batutuwan da suke tuhumar shugabannin ƙungiyar, akwai lokacin da ƴaƴan ƙungiyar sukayi aikin tafiye – tafiye zuwa ƙananan hukumomin Kano, inda sukayi aikin fito da nasarorin da gwamnatin jihar Kano ta samu a ɓangaran ilimi.

Takar ta cigaba da cewa ƴaƴan ƙungiyar sun samu labarin an basu naira miliyan biyar kuɗin aikin da sukayi, sai dai har yanzu basu san yadda akayi da kuɗaɗen nasu ba.

Leave a Reply