Ƙwararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Zubairu Shaba ya rasu
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Allah ya yiwa kwararren dan jarida me daukar hoto, Malam Zubairu Shaba rasuwa.
Ya rasu a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano bayan fama da rashin lafiya.
Malam Shaba ya yi aiki da jaridun New Nigeria, Triumph Hotline Magazine Daily Trust, Market Magazine da sauran jaridu.
KU KUMA KARANTA:Babban mataimaki na musamman na Gwamnan Kano kan gidajen rediyo ya rasu
Ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa 13 da jikoki kuma tuni aka yi jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Shagari Quaters a jihar Kano.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa.