Ƙungiyoyin musulunci sun raba wa marayu 900 abinci kyauta a Katsina (Hotuna)

0
146

Daga Abbas Bamalli

A wani biki mai ƙayatarwa da aka gudanar a gidan marayu na Katsina, sama da marayu 900 ne suka sami farin ciki matuƙa a lokacin da suka samu liyafar cin abincin rana, wanda ƙungiyoyi masu zaman kansu na Musulunci na ƙasa da ƙasa suka yi shirya.

Amir Sultana daga ƙasar Turkiyya tare da haɗin gwiwar Munazzama Da’awa Al-Islam (MADA) daga ƙasar Sudan ne suka shirya taron tare da haɗin gwiwar ofishin uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Raɗɗa.

Shugaban ƙungiyoyi masu zaman kansu, Mufti Ahmed, ya bayyana cewa kimanin marayu 700 a ƙaramar hukumar Katsina da 200 a Jibiya ne suka ci gajiyar wannan kyakkyawan shiri.

Ahmed ya jaddada cewa manufarsu ita ce sanya murmushi a fuskokin marasa galihu, musamman marayu, da ke nuna irin yadda ƙungiyoyin ke gudanar da ayyukan jin ƙai.

KU KUMA KARANTA: Zulum ya raba wa iyalai dubu 40 tallafin abinci da kuɗi a Konduga

An samo kuɗaɗe don shirin ne ta hanyar gudumawa daga mawadata da ɗaiɗaikun mutane da suka amince da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Mufti Ahmed ya bayyana cewa, “Ta hanyar tallafin mun gina rijiyoyin burtsatse kusan 36 a wurare daban-daban a jihar.”

Ya ci gaba da cewa, “Yana daga cikin shirinmu na yin amfani da ragowar kuɗaɗen wajen sanya murmushi a fuskokin marasa galihu, musamman marayu a cikin al’ummarmu.

Wani ɓangare na ayyukanmu shi ne rarraba Alƙur’ani mai girma da kuma bayar da tallafin kuɗi ga marasa galihu.” Baya ga cin abincin rana, ƙungiyoyin sun kuma bayar da gudummawar dalar Amurka 400 ga marayun, wanda hakan ya ƙara haɓaka tasirin ayyukansu na alheri.

Alhaji Isah Muhammad-Musa, kwamishinan ayyuka na musamman, ya yaba da wannan mataki na ƙungiyoyi masu zaman kansu, inda ya ce hakan ya ƙarawa ƙoƙarin Gwamna Dikko wajen tallafawa marasa galihu da marayu a jihar.

Ya bayyana cewa, uwargidan gwamnan ta shirya yin irin wannan aikin na jin ƙai nan ba da jimawa ba, tare da ƙara azama wajen ɗaukaka masu buƙata a cikin al’umma.

Kalli hotona a nan:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here