Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yaba wa Gwamnatin Zamfara kan ƙarin Albashin Likitoci

0
96
Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yaba wa Gwamnatin Zamfara kan ƙarin Albashin Likitoci

Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yaba wa Gwamnatin Zamfara kan ƙarin Albashin Likitoci

Daga Idris Umar, Zariya 

Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) Ta Yaba wa Gwamnatin Zamfara Kan Ƙarin Albashin Likitoci – Tace Likitocin Zamfara ne Zasu Karɓi Albashi Mafi Tsoka a Duk Arewacin Najeriya.

Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa amincewarsa da ƙarin albashi ga likitocin jihar Zamfara.

A cewar NMA, wannan ci gaba ya sa likitocin Zamfara suka zama mafi samun albashi a Arewacin Najeriya.

Shugaban ƙungiyar a jihar Zamfara, Dr. Ibrahim Hano, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis a Gusau.

Dr. Hano ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal wajen aiwatar da sauye-sauyen da ba a taɓa gani ba a sashen lafiya na jihar, yana mai bayyana gyaran da aka yi wa tsarin jin daɗin likitoci a matsayin kafa wani tarihi.

“Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta kafa sabon mizani ta hanyar amincewa da ƙarin albashi ga likitocin jihar, ciki har da aiwatar da tsarin ‘skipping’ da kuma bayar da ƙarin kuɗi ga likitocin da ke aiki a yankunan karkara.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana sabbin manufofi bayan taron Majalisar zartarwa

“Tare da wannan ci gaba mai daɗi, Zamfara yanzu ita ce ke biyan albashi mafi tsoka ga likitoci a Arewacin Najeriya,” in ji shugaban.

Ya ce wannan mataki zai ƙara wa ma’aikatan lafiya ƙwarin gwiwa, ya taimaka wajen hana su barin aiki, tare da jawo hankalin sabbin ma’aikata zuwa jihar.

Dr. Hano ya bayyana cewa ya na da yakinin cewa sauye-sauyen da Gwamna ke yi a bangaren lafiya za su zama abin koyi wajen samar da ingantacciyar kula da lafiya mai ɗorewa a jihar da ma yankin Arewa gaba ɗaya.

A cewarsa, Gwamnan ya cancanci yabo kan gyaran da ya yi wa Asibitin Kwararru ta Jihar da ke Gusau, da kuma asibitocin gwamnati da dama a faɗin jihar.

“NMA na matuƙar farin ciki da kayan aikin zamani da gwamnatin ta samar domin duba da kuma magance cututtuka masu tsanani a cibiyoyin kiwon lafiya.

“NMA kuma ta yaba da yadda wannan gwamnati ke fahimtar muhimmancin lafiyar matakin farko (primary healthcare) a matsayin ginshikin lafiyar al’umma.

“Amincewa da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya daga fannoni daban-daban da aka yi kwanan nan wata manufa ce ta hangen nesa wadda za ta magance ƙarancin ma’aikata da ke addabar fannin lafiya,” in ji shi.

Leave a Reply