Ƙungiyar ASUU ta janye yajin aiki bisa sharaɗi

0
641

Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU ta sanar da janye yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi. Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban ƙungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar Juma’a, bayan da shugabannin ƙungiyar suka gana jiya da daddare a Abuja babban birnin kasar. Sai dai bai yi bayani kan sharudan da suka sa aka janye yajin aikin ba.

Tun da farko, kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta umarci ƙungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari ɗaukaka ƙarar da ta yi a gabanta.Tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar malaman jami’o’in gwamnatin tarayyar Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki, suna neman gwamnatin ta biya musu wasu buƙatu.

An daɗe ana kai ruwa-rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU kan biyan buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.

Buƙatun sun ƙunshi samar da wadatattun kuɗi wanda za a yi ayyuka domin farfaɗo da jami’oi. Akwai buƙatar biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekaru ba a biya su ba. Akwai batun samar da wani kwamiti da zai riƙa ziyartar jami’o’in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu. Sannan akwai saɓani kan sabon tsarin biyan albashi na bai-daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS.

Leave a Reply