Ƙilu taja bau: Hukumar kula da kafafen yaɗa labaran Nigeria NBC ta haramta saka waƙoƙin Gwanja

2
625

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Baya ga hukuncin da babbar kotun shari’a musulunci dake Bichi ta ɗauka kan wasu mawaƙa ciki har da Ado gwanja, mai shari’a alkali Dr bello Musa Khalid yayi Wani hukunci akan wasu mutane da aka shigar da ƙara akansu.

Mutanen da aka shigar da ƙara akansu sun haɗa da 442 da kuma safara’u da Dan maraya sai kuma Amude booth da Kawu Dan sarki sai Kuma Ado Isa Gwanja da Kuma Murja ibrahim Kunya da Kuma Ummi Shakira da Samha M Inuwa da kuma uma Babiyana.

Da yake yanke hukunci akan waɗanda ake ƙara agaban kotun, Mai shari’a Dr bello Musa Khalid ya umarci kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da ya gaggauta kama waɗanda akayi ƙara da kuma gudanar da bincike akan dukkanin zarge zarge da ake yimusu.

Daga cikin abubuwan da akayi ƙara akansu sun haɗa da wasu waƙoƙi da sukayi karo da addini da kuma al’ada, masu suna ‘war’ da kuma ‘chas’ wanda Ado Isa Gwanja yayi, sai kuma sauran da ake zarginsu da hawa kan waƙoƙi Suna tiƙar rawa a tiktok, da kuma wasu abubuwa da sukayi karo da addinin musulunci da kuma al’ada.

Waƙar ‘war’ da kuma ‘chas’ ta janyo cece kuce a tsakanin al’umma wanda kuma hakan yasanya waɗannan lauyoyi shigar da ƙorafinsu gaban kotun.

Itama hukumar dake kula da kafafan yaɗa labarai ta Nigeria NBC ta haramta sa waƙoƙin Ado gwanja adukkan kafafan yaɗa labarai.

2 COMMENTS

Leave a Reply