Ƙarin bayani game da banbancin ‘Privatising’ da ‘Commercialising’ ɗin NNPC, daga Bashir Mahmood Baffa

0
677

Muna zaune da yamma a ƙofar gida na, sai aboki na Ahmad ya ce da ni, “naji ance wai ba PRIVATISING din NNPC aka yi ba, an dai yi COMMERCIALISING din sa ne. Ko me hakan yake nufi?”

Na ɗaga kai na kalle shi nace masa “eh, hakan yana nufin cewa gwamnati bata siyar da kamfanin ko wani sashe nashi ba ga yan kasuwa, har yanzu yana ƙarƙashin ikon gwamnatin Najeriya.

Ahmad ya sake tambaya ta “to menene bambamcin da aka samu a kamfanin tunda kace har yanzu yana ikon gwamnatin.” Sai nace masa “bambancin da aka samu na yanayin gudanarwa ne da kuma burin da gwamnati take nufin ta cimma akan kamfanin ne ya canza. Domin kafin ayi COMMERCIALISING din NNPC din, burin ba na samun riba bane, burin bai wuce na amfanuwar yan ƙasa ba, a samarwa mutane mai a farashi mai rahusa ba tare da wahala ba, kuma gwamnati ce take biyan albashin ma’aikata ta biya dukkan sauran kuɗaɗen gudanarwa ko anci riba ko ba a ci riba ba.

A yanzu kuwa burin gwamnati akan kamfanin na samun riba ne da rage kashe kuɗaɗe da asara yayin gudanarwa, sannan alhakin biyan albashi da kudin gudanarwa ya bar wuyan gwamnati ya koma kan kamfani, sannan zasu biya gwamnati haraji kamar yadda sauran kamfanoni ke biya.”

Sai Ahmad yace “to shin wannan abu ne mai kyau ko kuwa?”Sai nace masa “ya danganta da ta mahangar da ka kalle shi. Idan ka kalle shi ta mahangar da yan kasa da walwalar rayuwar su, ka iya cewa walwalar su zata ragu saboda farashin mai zai karu saboda tallafin da gwamnatin ke bayarwa ba zai samu ba domim burin shine a samu riba bayan biyan ma’aikata da kudin gudanarwa, wanda haka zai iya kawo dagawar farashin man kamar yadda muka fara gani yanzu.’

Na cigaba da cewa, “in ka kalle shi ta mahangar gwamnati amma, ka iya cewa abu ne mai kyau, saboda nauyin da ke kan gwamnati na albashi da sauran kudaden gudanarwar kamfani da tallafi da take biya duk zai ragu sannan zata samu kudin shiga ta fannin riba da haraji, wanda zata iya amfani dashi gurin yin wasu ayyukan gina kasa.”

Ta mahangar kamfanin kansa kuwa, a mahanga daya, abu ne mai kyau, a dayar mahangar kuma abu ne mara kyau. Kamar ta bangaren shugabancin kamfanin, abu ne mai kyau saboda zai sa kamfanin ya mai da hankali gurin yin aiki tukuru cikin karancin kashe kudi (da lokaci) wanda zai taimaka gurin ci gaban kamfanin. Ta fannin ma’aikata kuma, za a iya samun damuwa, saboda akwai yiwurar rage ma’aikata ko ragin albashin su don samun saukin kashe kudi da asara.”

Ahmad yace “to daga bayanan nan da kayi duka, COMMERCIALISATION, abu ne me kyau, ko mara kyau?” Na dan nunfasa, sannan nace masa, “bazan iya ce maka abu ne mai kyau ko mara kyau ba kai tsaye, abinda na fada maka amfani da kuma matsaltsalun da za a iya samu ne, amma babbar tambayar ita ce “me gwamnati zata yi da ribar da sauran kudaden da aka samu daga yin hakan? Idan kudin da aka samu din gwammati zata yi amfani da shi gurin samar da ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da tituna da sauran su, to abu ne mai kyau domin ta haka, amfanin abin zai rinayi rashin amfanin sa. Amma idan kudaden suka kare a aljihun wasu tsirarai ko a asusun banki wasu a kasar waje, to ma iya cewa kwalliya bats biya kudin sabulu ba.”

Daga Bashir Mahmood Baffa. Malami kan harkokin kasuwanci a Jami’ar Tarayya ta Dutse, Jihar Jigawa. Email:bmahmood03@gmail.com
Waya: 08038796815

Leave a Reply