Ƙarancin man fetur: NUPENG ta gargaɗi direbobin tankar manfetir

0
570

Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da albarkatun ƙasa ta Najeriya NUPENG, ta umurci direbobin tankokin mai, PTD, da sauran masu ruwa da tsaki wajen rabon manfetir da da su kasance a wuraren aikinsu ba dare ba rana, domin tabbatar da rarraba mai a duk faɗin ƙasa.

Haka zalika ƙungiyar ta kuma umarci ma’aikatan gidajen man fetir da gidajen mai da su yi watsi da duk wani nau’i na zamba cikin aminci ko rashin gaskiya da zai haifar ko ƙara taɓarɓarewar ƙarancin mai a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar ta NUPENG, Williams Akporeha, wanda ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a, ya sanar da cewa, hakan ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki ne da aka gudanar, don tabbatar da yadda ake rarraba mai a ko’ina a faɗin ƙasar nan.

A cewarsa, “ daga taron masu ruwa da tsaki na bangaren manfetir na masana’antar mai da iskar gas, ƙungiyar ma’aikatan manfetir da iskar gas ta Najeriya NUPENG ta sake umartar dukkan mambobinta da ke da ruwa da tsaki wajen rabon kayayyakin kai tsaye, musamman direbobin tankokin mai da ma’aikatan Depot, da ma’aikatan gidan mai, da su guji duk wani nau’i na haram ko almundahana da zai haifar ko kara karanci manfetir da ake fama da shi a kasar nan.

KU KUMA KARANTA:Kamfanin NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

“An kuma umurci dukkan membobin da su zama suna nan a wuraren lodi da rarrabawa wurare daban-daban a kowane lokaci don tabbatar da isasshen man, kuma ba tare da cikas ba, na rarraba albarkatun man fetir a cikin lunguna da sako na kasar.” In ji shi.

Tun da fari dai hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta baiwa kamfanin mai na NNPC da ‘yan kasuwar sa’o’i 48 domin su samar da man fetur ga ‘yan Najeriya

Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja bayan shafe sa’o’i uku ana ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur.

Ya ce rashin bin umarnin hukumar, DSS za ta fara gudanar da ayyukanta a fadin kasar nan.

A cewar Afunanya, ƙalubalen karancin man fetur ya dauki wani mataki da ke kawo illa ga tsaron kasar.

Ya ce a yayin taron, NNPC ta amince cewa akwai isassun manfetir da za su wadata ‘yan Nijeriya a lokacin bukukuwan karshen shekara da na sabuwar shekara.

Makwanni da dama, masu motoci musamman a Legas da Abuja sun sha wahala wajen samun man fetur daga gidajen mai, yayin da wasu gidajen mai a rufe, ‘yan kaɗan da ke buɗewa suna sayar da mai, a kan Naira 250 akan kowace lita ɗaya daga farashin asali na N169/lita.

Karancin wadatar ya janyo dogayen layukan a ’yan budaddiyar gidajen mai a yayin da masu ababen hawa da ‘yan kasuwa ke yunƙurin siyan mai yayin da wasu ke shiga kasuwar ‘yan bumburutu.

Lamarin ya kuma ƙara dagula cunkoson ababen hawa a manyan tituna, yayin da masu ababen hawa suka toshe akalla titin daya domin shiga jerin gwano zuwa gidajen mai.

Leave a Reply