Ƙarancin ma’aikatan tsaro, makaman yaƙi na zamani, rashin horaswa ne matsalar murƙushe ta’a’ddanci a Nijeriya, daga Dahiru Suleiman Dutse

0
487

Wani masanin harkokin tsaron ƙasar nan, Dokta Yahuza Getso (Mai ritaya), ya lura da cewa ƙarancin maaikatan tsaron ƙasa, da ƙin ba sojoji makaman da ya dace, da rashin tura su kwasa- kwasan Sanin makamar yaki da tinkarar abokanen gaba ne ummul haba’i’sin kasa shawo Kan matsalar tsaro a Nijeriya.

Dokta Getso na faɗin hakan ne a tattaunawarsu da wakilinmu a garin Dutse, inda ya nuna takaicinsa da yawaitar ayyukan taddanci babu ƙaƙƙautawa, inda ya dora alhakin hakan a kan sakacin mahukunta, a sabili da rashin gaskiya da adalci.

Ya ƙara da cewa, “da akwai ban takaici ganin yadda ba mu da wadatattun sojoji a ƙasar nan da za su iya murƙushe ayyukan taddanci cikin ƙanƙanin lokaci a sabili da kwadayi, zalunci, da son zuciyar wadanda alhakin kula da wannan bangaren ya rataya a wuyansu.

“Adadin sojoji da ‘yan sandanmu ba su gaza fiye da mutum dubu hamsin ba, ga shi Kuma an ƙi ba su makaman da ya dace a ba su a sabili da munafunci, cin hanci da rashawa, gami da son zuciya, to ta yaya za su iya tinkarar abokanen gabansu, wadanda ke dauke da muggan makamai, ga su Kuma da gogewar Sanin makamar yaki” in ji Dokta Getso.

Saboda haka acewarsa, “hanya ta farko da za ta wanzar da maslaha ga wannan ta’addanci ita ce, lallai mahukunta su ba da amincewar ƙarin daukar ma’aikata aikin soja, da na ‘yan sanda, da makamantansu. Ba ya ga haka, a rika ba sojojinmu makaman da ya dace, kuma irin na zamani, tare da ba su horo kan sanin sabbin dabarun yaƙi da fuskantar abokanen gaba akai akai.

“Ya zama wajibi mu ƙara ba sojojinmu kulawa ta sosai, musamman abin da ya danganci wadata su da isasshen kayan aiki, da kyakkyawan albashi, da yanayin wurin zama, ma’ana muhalli mai kyau.

“Muddin ba wadannan matakai muka runguma ka’i’n da naim ba, babu ta yadda za mu yi adabo da matsalar tsaro a Kasar nan”.

Leave a Reply